Yin aiki hour shida zuwa takwas ba abin wasa ba ne – Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yin aiki na tsawon awanni takwas a rana ba wasa ba ne a jikinsa.
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta kasa, NTA a ranar Alhamis.
Ya ce, “A game da shekaru na, na ga abokan aikina, yanzu suna hutawa, kuma ina tabbatar muku cewa ina sa ran nan da watanni 17 masu zuwa lokacin da ni ma ba zan shagala ba.
“Shekaru ya nuna min, yin aiki yanzu na tsawon awanni shida, bakwai zuwa takwas a kowace rana a ofis ba abin wasa ba ne, akwai tambayoyin majalisar zartarwa, rubutattun bayanai daga jihohi da dama da za a yi la’akari da su kusan kowane mako.
"Hakika, aiki ne mai wuyar gaske, amma bari mu ce, na nemi hakan kuma ba zan iya yin korafi ba."
Janar din mai ritaya ya kara da cewa, “Ni na zama gwamna, na yi minista, kuma ina cikin wa’adina na biyu a matsayin shugaban kasa. Don haka, na bi duk tsarin kuma da gaske, me kuma zan iya yi wa kasar nan? Na yi iya kokarina kuma ina fata bayan na tafi, 'yan Najeriya za su yi tunani kuma a kalla su nuna godiya.
Comments
Post a Comment